Majalisar Najeriya ta ji bahasi kan Dokar NFF

Bolaji Abdullahi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ministan Wasanni na Najeriya, Bolaji Abdullahi

Majalisar Dokoki ta Najeriya ta gudanar da zaman jin bahasi a kan dokar da ta kafa Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa.

Masu ruwa da tsake da dama ne dai suka bayyana yayin zaman jin bahasin, wanda ya tattaro ra'ayoyi dangane da bukatar soke Dokar Hukumar Kwallon Kafa ta NFA ta 2004 da kuma maye gurbinta da Dokar Hukumar Kwallon Kafa ta NFF ta 2012.

Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai ta Najeriyar mai kula da Wasanni, Honourable Godfrey Gaiya, ya shaidawa BBC cewa:

"Mun kira jama'a ne domin kowa ya tofa albarkacin bakinshi game da tsarin da muke so mu kawo—janye Dokar Hukumar NFA ta 2004 da kuma maye gurbinta da Dokar Hukumar NFF ta 2012.

"Bayan haka mu daidaita tsarin gudanar da wasan kwallon kafa a Najeriya da wanda ake samu a ko'ina a duniya".

Daga cikin masu ruwa da tsakin da suka halarci zaman har da Shugaban Kwamitin Wasanni na Majalisar Dattawa, Sanata Adamu Gumba, da Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa, NFF, Aminu Maigari, da Kocin Super Eagles, Stephen Keshi, da tsohon Sakataren NFA, Alhaji Sani Toro.

Karin bayani