Tennis: Del Potro da Murray a Queen's Club

Juan Martin del Potro
Image caption Juan Martin del Potro

Dan Argentina Juan Martin del Potro zai bi sahun Andy Murray da Jo-Wilfred Tsonga a filin wasan tennis na Queen's Club don kece raini a Gasar AEGON a watan Yuni.

Dan wasan na goma sha daya a duniya, wanda ya lashe Gasar US Open a 2009, zai sake halartar gasar ta share fagen shiga Gasar Wimbledon ce a karo na uku.

Tuni dai dan Faransar, wato Tsonga, ya tabbatar da cewa zai kara kokari a kan wanda ya yi bara yayin neman gurbi a zagayen karshe na Gasar ta AEGON, inda ya sha kashi a hannun Murray.

Tsonga dai ya casa Roger Federer a kan hanyarsa ta zuwa zagayen kusa da na karshe a Gasar Wimbledon, yana kuma fatan sake samun irin wannan nasara a 2012.