Magoya baya ne suka ba mu kwarin guiwa - Blackburn

Shugaban klub din Balckburn, Steve Kean Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban klub din Balckburn, Steve Kean

Shugaban klub din kwallon kafa na Blackburn Steve Kean yace karin hadin kan 'yan wasa ne ya yi sanadiyyar nasarar da klub din ya samu sau uku a baya-bayan nan a wasanni biyar da suka buga.

Nasarar ci biyu ba ko daya da klub din na Blackburn Rovers ya samu akan klub din Sunderlands ne ya kai ga nasarar da Rovers suka samu a jere kuma a karo na farko a lokacin shugabancin Kean.

Kean ya shaida wa BBC cewa "Ina ganin masoya wasanmu na samun sakamakon da ya cancanta na goyon bayan da suke baiwa 'yan wasanmu."

"Mu gudu tare, mu tsira tare, amma a yanzu sun fara ganin hazakarmu."

'Yan wasa Rovers, Junior Hoilett da Yakubu ne suka zura kwallaye a ragar Wolves, abinda ya kai ga samun nasarar da Blackburn ta yi a wasan da suka buga kwana goma da suka wuce.

Hakan dai ya daga likkafar klub din Kean da maki shida daga komawa rukuni na kasa a gasar Premier.

Hakan kuma na zuwa ne bayan masoya klub din da fari sun yi wani bore suna masu kira da Kean da kuma Ba- Indiyen dake da klub din Venky da su bar klub din da ke yankin Lancashire.

Nasarar da Blackburn ya samu kan Wolves ya kawo kyakkyawan fata a kakar gasar wasanni na bana, kuma ya kara daga likkafar Kean wanda ya karbi ragamar jagorancin klub din a watan Disambar shekarar 2010.