Za a yi Gasar Kwallon Gora ta Turai a Ingila

'Yan wasan gora Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan wasan kwallon gora na Turai

Ingila za ta karbi bakuncin Gasar Kwallon Gora ta Turai ta 2015 a Dandalin Gasar Olympic ta bana a birnin Landan.

Wannan ce dai gasar kasa-da-kasa ta farko da za a yi a dandalin bayan gudanar da Gasar Olympics ta Landan ta 2012.

Duk wadanda suka yi nasara, maza da mata, suna da tabbacin samun gurbin zuwa Gasar Olympics ta 2016 a Brazil.

A farko wannan watan ne aka yanke shawarar gudanar da gasar a Cibiyar Kwallon Gora ta Lee Valley da ke Dandalin Gasar ta Olympic yayin wani taron kwamitin gudanarwar Hukumar Kwallon Gora ta Turai a Bratislava da ke kasar Slovakia.