Messi ya kafa tarihin zura kwallo

Hakkin mallakar hoto Getty

Lionel Messi ya kafa tarihi na zura kwallaye da ba'a samu irinsa ba a shekaru sittin da suka gabata a klub din Barcelona.

Messi ya kafa tarihin ne bayan zura kwallaye uku a wasan da Barcelona ta doke Granada a Nou Camp da aka tashi ci biyar da uku a gasar La Liga ranar Talata.

Kwallon da Messi ya zura a mintuna 17 da fara wasan ne yasa ya yi daidai da tarihin da aka kafa a shekaru sittin da suka wuce, sannan ya kara zura wata a mintuna 68 abinda ya kaishi kafa sabon tarihi.

An dai rage darajar tarihin da ya kafa zuwa 232 daga 235 bayan wani nazari da wata jarida ta yi.