Muamba ya yi minti 78 'kusan a mace' —Likita

Fabrice Muamba Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Dan wasan Bolton, Fabrice Muamba, kafin ciwon zuciya ya kama shi

Likitan kungiyar kwallon kafa ta Bolton Wanderers, Jonathan Tobin, ya ce Fabrice Muamba ya shafe minti saba'in da takwas 'kusan a mace' bayan ya yanke jiki ya fadi a filin wasa.

Likitoci dai sun ce lokaci bai yi ba tukunna da za a iya hasashen ko Muamba zai iya ci gaba da buga kwallo ko a'a.

Sai dai Dokta Tobin ya ce ya yi mamakin saukin da dan wasan ya samu ya zuwa yanzu.

"Ina farin cikin tabbatar da cewa alamun samun sauki sun ci gaba da bayyana; na je na ga Fabrice—da na shiga sai ya ce min 'Yaya aka yi ne dokta?' Na tambaye shi 'Yaya jiki?' Sai ya ce 'Da sauki'. Ya kuma tambaye ni abin da ya faru, na yi masa bayani", in ji Dokta Tobin.

A halin da ake ciki kuma, ranar Asabar kungiyar ta Bolton Wanderers za ta koma bakin daga bayan da iyalan Muamba suka shaidawa kungiyar cewa za su so ta ci gaba da buga wasanninta.

Don haka ne ma kungiyar za ta buga wasanta da Blackburn Rovers ranar kamar yadda aka shirya da misalin uku na rana agogon GMT.

Kungiyar ta Bolton ta kuma tabbatar da cewa za ta sake buga wasanta na daf da na kusa da na karshe a Gasar Cin Kofin FA da Tottenham Hotspur.

Karin bayani