Yakin cacar bakan Man City da Man Utd

Sir Alex Ferguson Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson ya yi suka ga klub din kwallon kafa na Manchester City, bayan United ta yanke shawarar katse ritayar Paul Scholes.

Tsohon dan wasan tsakiya na klub din Chelsea, Patrick Viera yace yunkurin wani "rauni" ne.

Sai dai Ferguson ya yi gargadin cewa Idan abokan hamayyarsu Man City na son ayi yakin cacar baka ne to " Na shirya makamai na masu yawa"

" Idan har mun shiga halin rashin ta yi ne ya sa za mu dawo da kwararren dan wasan tsakiya a Burtaniya a shekaru 20 da suka wuce, to ina ganin zan iya amincewa da haka" Inji Ferguson.