Kan magoya bayan Real Madrid ya daure

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo

Real Madrid ta fusata bayan da alamu suka nuna cewa dan wasan gaban Villareal, Marco Ruben, ya ci gaba da kasancewa a cikin fili duk da cewa alkalin wasa ya daga masa kati mai ruwan dorawa har sau biyu a wasan da kungiyoyin suka buga ranar Laraba, wanda aka tashi kunnen doki daya da daya.

A bangaren Real Madrid din dai an kora kocin kungiyar, Jose Mourinho, da mai kula da lafiyar 'yan wasa, Rui Faria, cikin 'yan kallo, yayin da daga baya aka sallami Mezut Ozil da Sergio Ramos.

Rudanin dai ya taso ne dangane da katin da aka baiwa Marcos Senna wanda ba ya kusa da alkalin wasa yayin da aka ga Cani da Ruben suna nuna rashin jin dadinsu a kusa da alkalin wasan.

Wata ruwayar dai cewa ta yi Sennan ya nuna bacin ransa ga alkalin wasa sannan ya nufi gefen fili, alkalin kuma ya ba shi kati ne yayin da juya baya.

Sai dai 'yan kallo sun rude suna tunanin Ruben aka baiwa katin.

Don haka ne lokacin da aka baiwa dan wasan kati a minti na hamsin da biyar (a tunanin wasu a karo na biyu) ba a ba shi jan kati ba, magoya bayan Madrid suka cika da ta'ajibi, musamman ma ganin daga baya an sallami Ozil, da Ramos, da Rui Faria, da Mourinho.