Rangers ta bada mamaki a karawarsu da Celtic

Karawar Ragers da Celtic Hakkin mallakar hoto bestpix
Image caption Karawar Ragers da Celtic

Yan wasan dake tashe wato Rangers sun hana Celtic daga kofin Scotland, duk da matukar kokarin da Celtic din suka yi don su samu nasara.

Celtic dai ta kasance ne da yan wasa tara kacal a filin wasan, kuma ta kwashi kashinta a hannu da ci ukku da biyu.

Sone Aluko ne ya fara fasa ragar Celtic, sannan sai Andy Little, daga nan sai Celtic ta rama ci guda yayinda Lee Wallace ya kara daya. Celtic ta yunkura ta farke ci biyu amma, har aka tashi, da ci ukku da biyu.

An kori Cha Du-Ri bayan mintuna 29 da fara wasan, yayinda Victor Wanyama ya biye masa, wanda ya maida Celtic da yan wasa 9 kacal.