Fabrice Muamba zai iya tashi daga gadonsa na asibiti

Fabrice Muamba ya fara farfadowa
Image caption Fabrice Muamba ya fara farfadowa

Dan wasan tsakiya na kulob din kwallon kafa na Bolton Fabrice Muamba ya farfado, kuma a yanzu zai iya zama a kan gadon sa na asibiti, har ma ya na cin abinci da kallon yan kulob din sa a wasan da suka buga.

Wata sanarwar ta hadin gwiwa tsakanin hukumomin asibitin da yan kulob din na Bolton na cewa, ya na ci gaba da samun sauki sosai.

Manajan kulob din Owen Coyle ya ce Muamba ya kalli takaitaccen labarin wasan da Bolton ta yi nasara kan Blackburn da ci 2 da daya a ranar Lahadi.

Ya ce wani abin kwantar da hankali da nishadi shine, ya yi barci a lokacin da Bolton ke da ci biyu da nema.