Shooting stars ta dakatar da mai horar da yan wasan ta

yan wasan 3 SC Hakkin mallakar hoto super sports
Image caption yan wasan 3 SC

Daya daga cikin manyan kulob din kwallon kafa a Nigeria wato Shooting Stars ta bada sanarwar dakatar da kocin kulob din Festus Allen har sai abin da hali yayi.

Kulob din ta ce ta dauki wannan matakin ne saboda irin muguwar rawar da ta taka a karkashin jagorancin sa a gasar kulob kulob na kasar.

A ranar Lahadi ne kulob din na Shooting Stars ya kwashin kashinsa a hannu wurin Kaduna United, karo na ukku a jere.

A halin yanzu dai su ne na 18 a cikin kulob 20 dake taka leda a wasannin League, inda suke da maki 17 a wasanni 16 da suka buga.