Babatun da Drogba yayi, ya harzuka Benfica

Didier Drogba Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Didier Drogba

Mai horar da yan wasan kulob din Benfica ya sha alwashin maida martani game da babatun da ya ce Drogba ya yi, ta hanyar lallasa Chelsea.

A wani hoton bidiyo na shafin internet din Chelsea, an nuno Drogba ya na kwaikwayon yadda bangaren kasar Portugal suka tsorata da Chelsea.

Mai horar da yan wasan na Benfica, Jorge Jesus ya yarda cewa Drogba wasa yake yi, to amma ya kara da cewa, Drogba ne kadai ya san abin da ya ke cikin zuciyar sa.

Chelsea dai ta ce, an samu rashin fahimta ne game da batun, to amma babu yadda za a yi ta dau Benfica sako-sako, don a cikin wasannin da ta buga guda goma babu inda aka doke ta, saidai kunnen doki.