"babu wanda bai samun sa'a a wasa", inji Ferguson

Sir Alex Ferguson Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sir Alex Ferguson

Mai horar da yan wasan kulob din Manchester United Sir Alex Ferguson ya hakikance cewa, matakin da alkalan wasa ke dauka masu takaddama, kan faru ga kusan kowa, a kakar wasanni.

An hana kulob din Fulham bugun daga kai sai gola ne a wasan da Mancheter United ta yi nasara da ci daya da nema a Old Trafford, inda ta samu damar zarce Manchester City da maki ukku a gasar Premier.

Ferguson ya ce kowa kan samu irin wannan fifiko a kakar wasa, kuma babu abin da zai taba sauyawa.

Za ka iya samun fifiko nan da can. Babu kulob din da ba ta samun irin wannan dama, masu kyau da marasa kyau. Inji Ferguson.

Fulham dai ta so a ba ta panaret, ana saura yan mintuna kadan a kammala wasan, amma alkalin wasan, ya kauda kai.