Rangers na farautar dan kallon da yayi jifa da kwandala

Qweens Park Rangers
Image caption Qweens Park Rangers

Kulob din Queens Park Rangers ya yi kira ga dukkanin magoya bayan kulob din da su nuna dan kallon da ya jefi mataimakin alkalin wasa Stuart Burt da kwandala.

A cikin wata sanarwa da mahukunta a kulob suka yada ta kafar sadarwa na twitter, sun ce kulob din na sane da batun jifa da kwandala wanda ya auku a karshen wasan da suka buga da Arsenal a ranar Asabar.

An harbi Burt ne a bayan wuyan sa ta hanyar jifa daga cikin yan kallo, bayan da ya baiwa Arsenal bugun tazara ana cikin karin lokaci.

Rahotanni na nuna cewa hukumar kwallon kafar Ingila ta san da lamarin kuma ta na goyon bayan kokarin kulob din Queens Park Rangers da yan sanda don hukunta wanda ya yi wannan jifa, wanda ka iya fuskantar haramci na illa masha Allahu daga filin wasan.