Russia za ta dau mataki kan wanda ya jefi Samba da ayaba

Christopher Samba Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Christopher Samba

Hukumar kwallon kafar Russia na neman daukar matakin shariah kan dalibin da ya jefi Christopher Samba dan kasar Congo kuma dan wasan kulob din Anzhi Makhachkala, da ayaba.

Shugaban kwamitin da'a na hukumar kwallon kafar Russian ya yi kiran da a dauki mataki kan dalibin da ya yi jifan na ranar 20 ga watan Maris, bayan da aka gano shi a makon jiya.

Shugaban kwamitin da'ar Vasilev Vladimir ya ce sun aika da sakamakon binciken su ga hukumomin shariar kasar.

Tsohon dan wasan baya na kulob din Blackburn Rovers, wato Samba, na kan hanyar sa ce ta zuwa dakin janza kaya bayan hura usur na karshe a wasan su da Lokomotiv Moscow, inda aka ci Anzhi daya da nema, aka jeho wata ayaba ta fadi a kusa da shi.

Shi kuma dan shekaru 27n ya dauki ayabar ya jefa ta inda ta fito, inda ya ce ya na fata wannan za ta zama misali na irin halin da bai dace ba.