Samuel Eto'o na Kamaru ya janye karar da ya kai Barcelona

Samuel Eto'o Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Samuel Eto'o

Dan asalin kasar Kamaru Samuel Eto'o ya janye karar da ya kai tsohon kulob din sa na Barcelona kan kudaden da ya yi ikirarin cewa ya na bin kulob din, a lokacin komawar sa Inter Milan.

A baya dai dan wasan gaba Samuel Eto'o ya bukaci kusan dala million 4, a yarjejeniyar da suka kulla ta shekarar 2009.

A na ta martanin, kulob din Barcelona ta bayyana godiyar ta ga Samuel Eto'o na amincewar da ya yi ya kawo karshen wannan takaddamar.

Kyaptin din yan wasan Kamaru na Indomitable Lions, wanda yanzu ya ke kulob din Anzhi Makhachkala ta kasar Russia, ya koma Inter ne a karkashin yarjejeniyar musayar yan wasa tsakaninsa da Zlatan Ibrahimovic.

Karin bayani