Chelsea kulob ce mai karfi a duniya, inji di Matteo

Roberto di Matteo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Roberto di Matteo

Mai horar da yan wasan kulob din Chelsea na riko Roberto di Matteo ya yi imanin cewa kulob din sa na da karfi a duniya, duk kuwa da cewa bai taba daga kofin wasan zakarun turai ba.

Idan Chelsea ta yi nasara kan Benfica a daren yau Laraba, za ta shiga zagayen kusa da na karshe a karo na shidda cikin kakar wasanni 9.

Di Matteo ya ce, idan ka duba shekaru goma da suka gabata, Chelsea ta na da karfi sosai a cikin gida da ma duniya baki daya.

Dan wasan tsakiya na kulob din Ramires ya bayyana cewa, ana ganin kulob din a matsayi irin na su Barcelona da Real Madrid a kasashe irin su Brazil.

Karin bayani