Portsmouth na fuskantar durkushewa

kulob din Portsmouth Hakkin mallakar hoto
Image caption kulob din Portsmouth

Magoyabayan kulob din Portsmouth na bukatar samar da pan million 8 don ceto kulob din daga durkushewa.

A baya bayan nan ne kulob din ya kaddamar da hannayen jarin sa ga magoya bayan kulob din da su sanya pan 100 a cikin wani asusu wanda za a biya su daga baya don karfafa kulob din.

Idan aka samu mutane da yawa da suka sanya kudi a cikin asusun, kungiyar magoya bayan kulob din za su iya bada tayin su na siyan kulob din na Portsmouth.

Kakakin kungiyar magoya bayan kulob din Scott Mclachlan ya ce su na bukatar samar da pan million 8, kuma ba dole ne dukkanin kudaden su fito daga hannayen jarin kulob din ba.

A halin yanzu dai hukumomi na sanya ido kan kulob din na Portsmouth kuma su na fuskantar fita daga matakin farko a wasannin League, baya ga haka kuma, idan kulob din bai samu mai siyan sa ba kafin nan da yan watanni, kulob din zai durkushe.

Karin bayani