Masar ta gayyaci 'yan wasa 73 domin Olympics

Tawagar Masar
Image caption Masar na fuskantar koma baya a 'yan kwanakin nan

Kocin 'yan kwallon Masar na 'yan kasa da shekaru 23 Hany Ramzy ya gayyaci 'yan wasa 73 domin shirye-shiryen gasar kwallon kafa ta Olympics.

Domin tantance 'yan wasan, an shirya cewa tawagar za ta yi wasannin sada zumunci 14 tsakanin 15 ga watan Afrilu da 19 ga watan Yuli.

Tawagar ta hada da shahararrun 'yan wasa kamar Ahmed Hassan, Mohamed Aboutrika da Essam El Hadary.

Ramzy yana da damar sanya 'yan wasa uku da shekarunsu suka haura 23 a cikin tawagar.

A yanzu haka 27 daga cikin 'yan wasan suna Costa Rica domin yin atisayi inda za su kara da Uruguay a wasan sada zumunta.

Suna kuma saran shirya wasu wasannin da Panama da Honduras.