Mancini ya fitar da rai da daukar Premier

Roberto Mancini
Image caption Mancini ya ce aikin gama-ya-gama game da Premier

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya ce kulob dinsa ba zai lashe gasar Premier ta bana ba, duk kuwa da ssun rage tazarar da Man United ta basu zuwa maki biyar.

City ta lallasa West Brom da ci 4-0 ranar Laraba, yayin da United ta sha kashi da ci daya da nema a hannun Wigan, abinda ake ganin ya baiwa City karin dama.

"Aikin gama-ya-gama," a cewar Mancini. "Maki biyar yayi yawa".

"Manchester United na da zuciya da karfin hali. Irin karfin halin da mu kuma muka rasa."

Kocin dan kasar Italiya ya ce yana so ne Man City ta kare kakar bana cikin nasara kamar yadda suka fara.

"Ina ganin kamata yayi mu kammala kakar bana cikin nasara," acewar Mancini, wanda kulob dinsa zai karbi bakuncin United a ranar 30 ga watan Afrilu. "Wannan ita ce kakar wasanninmu mafi kyau a cikin shekaru 50 kuma ina alfahari da 'yan wasa na."

Karin bayani