Har yanzu Rangers na tsaka mai wuya

Image caption Rangers ta kara dilmiya cikin matsala

Kungiyar kwallon kafa ta Rangers na iya fara wasannin kaka biyu a nan gaba da ragin maki goma idan aka sayarda ita.

Hukumar gasar wasan Premier ta Scotland za ta duba wasu sabbin ka'idoji da za a duba yuwuwar amfani da su wadanda suka danganci kudade a wani taro da za ta yi ranar 30 ga watan Afrilu.

Kungiyar Rangers wadda yanzu ta ke cikin matsalar kudi tana fuskantar durkushewa wanda hakan ke nufin kila ta maida kadarorinta ga wani sabon kamfani da zai mallake ta.

Masu kamfanin da ke kula da harkokin kungiyar ta Rangers, Duff & Phelps sun ce sanarwar sabbin ka'idojin ta kawo jinkiri wajen sayarda kungiyar.

Bisa tanadin sabbin ka'idojin na hukumar wasannin Premier ta Scotland, za a yankewa kungiyar da ta sami kanta cikin matsalar kudade maki 15 maimakon 10 da ake cirewa a yanzu.