Muna son Wenger ya ci gaba da zama - Arsenal

Arsene Wenger
Image caption Arsene Wenger ne kocin da ya fi dadewa a tarihin Arsenal

Shugaban kulob din Arsenal Peter Hill-Wood ya ce zai so kocin kulob din Arsene Wenger ya tsawaita kwantiraginsa, wacce za ta kare a watan Yunin shekara ta 2014.

Kocin wanda a 'yan watannin da suka wuce ake batun korarsa, ya farfado da martabarsa tsakanin magoya bayan kulob din, sakamakon wasu nasarori da ya samu.

Hill-Wood ya bi sahun magoya bayan Arsenal wurin nuna sha'awar kocin dan kasar Faransa ya ci gaba da zama a Arsenal .

Ya shaida wa jaridar Daily Mirror cewa: "Babbar nasara ce idan ya ci gaba da zama a kulob din har fiye da shekarar 2014. Ba na ganin akwai wanda ya fi shi cancanta ya jagoranci kulob din.

Ya soki mutanen da ke cewa Arsene Wenger ba ya tafiya da zamani don haka kamata ya yi a kore shi.

Haskakawar da Arsenal ke yi a yanzu ta sa sun koma mataki na uku a teburin Premier inda suka haye saman abokan hamayyarsu Tottenham da kuma Chelsea.

"Yana da matasan 'yan wasa, masu hazaka da kwarewa," a cewar Hill-Wood.