Formula 1: Nico Rosberg ya lashe gasar China

Nico Rosberg Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wannan ne karon farko da ya lashe gasar Grand Prix

Nico Rosberg ya lashe gasar tseren motoci ta Chinese Grand Prix da aka fafata a China a karon farko a tarihinsa.

Dan wasan na kasar Jamus ya mamaye tseren tun daga farko har karshe, musamman bayan da aka dan dakatar da Jenson Button na McLaren a yunkurinsa na karshe.

Wannan ne karon farko da tawagar Mercedes ta lashe tseren tun shekarar 1955 a gasar Italian Grand Prix.

Batun ne ya zo na biyu bayan ya doke abokin wasansa Lewis Hamilton da Mark Webber na Red Bulls da kuma Sebastian Vettel.

Romain Grosjean na Lotus ne ya zo na shida, a saman Bruno Senna da Pastor Maldonado na Williams da Fernando Alonso na Ferrari.

Sakamakon ya nuna cewa Hamilton ne kan gaba a baki dayan gasar inda ya haura Button da maki biyu. Sai Alonso da ke mataki na uku.