Ana zaman makokin Morosini a Italiya

 Piermario Morosini Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana nuna jimami kan mutuwar Morosini a sassa da dama na duniya

Jama'a a Italiya na bayyana jimaminsu game da mutuwar dan kwallon Livorno Piermario Morosini, wanda ya fadi lokacin da yake taka leda ranar Asabar.

An kuma bayyana jimamin a mafiya yawan jaridun kasar na ranar Lahadi.

Morosini ya rasa iyayensa biyu tun yana dan shekara 18, kuma daga bisani dan uwansa ya kashe kansa.

An dakatar da dukkan wasanni a kasar ta Italiya. Za kuma a gudanar da bincike kan dalilin mutuwarsa a ranar Litinin.

Morosini, mai shekaru 25, yana zaman wucin gadi ne daga kulob din Udinese lokacin da ya fadi a minti na 31 lokacin da yake taka leda a wasan Livorno da Pescara na Serie B.

Daga nan ne kuma aka garzaya da shi asibiti, inda kuma likitoci suka yi kokarin ceto rayuwarsa, amma ba tare da nasara ba.