An kama wani mutum bisa cin zarafin Balotelli

Mario Balotelli Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Mario Balotelli ya dade yana janyo cece-kuce

'Yan sanda sun kama wani mutum kan zargin batawa dan wasan Manchester City Mario Balotelli suna, amma daga bisani an bayar da belinsa.

Ana kyautata zaton lamarin ya shafi wasu hotuna ne da aka dauka a wani gidan rawa, kuma jami'an Man City ne suka shaida wa'yan sanda.

Mai magana da yawun 'yan sandan birnin Manchester ya ce: "'yan sanda na bincike bayan da Man City ta yi zargin an batawa dan wasan suna.

"An kama wani mutum amma an bayar da belinsa. Ana ci gaba da gudanar da bincike."

Ana kyautata zaton cewa an dauki hotunan da jaridu suka buga da ke nuna Balotelli dan shekaru 21, na shan giya, a gidan rawa na Panacea a ranar 11 ga watan Maris.

Tunda farko a ranar Manchester City ta rasa matsayinta na daya a kan teburin Premier bayan da suka sha kashi da ci 1-0 a hannun Swansea City.

Karin bayani