'Yan sanda sun kama El Hadji Diouf

El Hadji Diouf
Image caption El Hadji Diouf yana taka leda ne a Doncaster Rovers

An kama mutane shida ciki har da tsohon dan wasan Senegal El Hadji Diouf bayan da fada ya barke a wani gidan rawa a Manchester, inda mutum ya samu mummunan rauni.

Dan wasan na Doncaster Rovers mai shekaru 31, yana cikin mutane biyar din da aka bayar da belinsu har zuwa ranar 23 ga watan Mayu.

'Yan sanda sun kuma yiwa dan wasan QPR Anton Ferdinand mai shekaru 27, tambayoyi amma ba a kama shi ba.

Wani mutum mai shekaru 33 ya samu mummunan rauni amma yana kwance a asibiti, a cewar mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta Greater Manchester.

Lamarin dai ya faru ne ranar Lahadi da misalin karfe 03:40 a gidan rawa na Circle Club.

Sanarwar da 'yan sanda suka bayar ta ce: "An kama mutane shida bisa zargin tayar da hankali, an bayar da belin biyar daga cikinsu zuwa ranar 23 ga watan Mayu zuwa lokacin da za a kammala bincike.