Kwanaki 100 kafin fara gasar Olympics

 Haile Gebrselassie Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sau biyu Haile Gebrselassie yana zama zakaran wasan Olympics

A daidai lokacin da ya rage kwanaki 100 kafin a fara gasar wasanni ta Olympics, tsohon zakaran gudun fanfalaki na Olympics Haile Gebrselassie ya fitar da rai daga halartar gasar.

Gebrselassie mai shekaru 39 ya lashe lambar zinare sau biyu a gudun mita 10,000 kafin ya sauya sheka zuwa gudun fanfalaki a 2004.

Sai dai ya kasa samun gurbi a tawagar da za ta wakilci Ethiopia a gudun fanfalaki a gasar ta London 2012.

"Yawancin 'yan wasan Ethiopia sun yi gudun ne a minti 2:04 amma Haile ya kasa cimmusu.

Ya fitar da rai daga gasar Olympics ta London 2012 cikin damuwa da dimauta," a cewar manajansa Jos Hermans.

Dan wasan ya samu koma-baya a kokarinsa na shiga gasar ta London 2012 lokacin da ya zo na hudu a gudun fanfalaki na Tokyo a minti 2:08.17.

Goma sha takwas daga cikin abokan fafatawarsa sun yi gudun da ya haura nasa, abinda ya jefa kwararran dan wasan cikin tsaka mai wuya.

Gebrselassie ya nace cewa zai ci gaba da yin tseren gudu mai nisa, sannan ya tabbatar da cewa zai halarci gasar tseren Manchester da za a yi a watan Mayu.

Sau uku yana lashe wannan gasar a baya-bayan nan.

Karin bayani