Kociyan Botswana Tshosane bai gamsu dari bisa dari ba

Stanley Tshosane Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Stanley Tshosane

Kociyan Botswana Stanley Tshosane ya bayyana cewa bai gamsu sosai ba, duk da sa hannun sa a sabon kwantaragi na shekaru ukku, wanda ya kara waadin sa zuwa shekarar 2015.

A yayin da Tshosane zai samu ribin albashin sa zuwa dala dubu tara a ko wanne wata, garabasar yan wasa kuwa, har yanzu ita ce abar damuwa.

Ya ce na sanya hannu kan yarjejeniya ta shekaru ukku, to amma wannan ba ya na nufin cewa na gamsu da komi bane, dole ne a samar da maslaha a wasu batutuwa.

Tshosane da hukumar kwallon kafar Botswana sun fara tattaunawa ne kan sabon kwantaragin kafin fara wasan cin kofin Afirka wanda aka yi a farkon wannan shekara, to amma mai horar da yan wasan ya jinkirta sanya hannu a kai, bisa ikirarin da ya yi cewa babban abun damuwa shi ne albashin yan wasa.

Karin bayani