London 2012: Burtaniya "za ta lashe lambobin zinare 27"

Tawagar Burtaniya Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Tawagar Burtaniya ta zo ta hudu a gasar Olympics ta 2008 a Beijing

Tawagar Burtaniya za ta lashe lambobin zinare 27 a gasar Olympics ta bana, adadi mafi girma cikin shekaru, kamar yadda wani bincike da BBC ta gani ya nuna.

Wannan adadin zai iya sa Burtaniya ta zamo kasa ta uku a teburin lambar yabo a gasar ta London 2012, inda za ta shiga gaban Rasha.

Binciken na jami'ar Sheffield Hallam an gudanar da shi ne ta hanyar la'akari da kokarin da tawagar ta yi a baya da kuma damar da za su samu kasancewar su ne masu masaukin baki.

Lambobin 27 sun zarta sauran hasashen da aka yi a baya.

Alal misali kamfanin da ke gudanar bincike Infostrada, ta yi hasashen Burtaniya za ta lashe lambobin zinare 16 ne a gasar inda za ta zamo ta biyar a tebur, ta hanyar la'akari da bayanan da ta samu kan 'yan wasan a wasannin da suka buga na baya-bayan nan.

Luciano Barra, tsohon mamba a kwamitin Olympics na Italiya, tun watanni da dama da suka wuce ya yi hasashen cewa lambobi 12 Burtaniya za ta samu - duk da cewa ya dora hasashen ne kan nasarorin da aka samu a gasar world championship - amma yanzu ya karu zuwa 16.

Tawagar Burtaniya ta zo ta hudu a gasar Olympics ta 2008 a Beijing, inda ta lashe lambobin zinare 19.

An samu kari kan adadin da kasar ta samu a gasar da aka yi a Athens shekaru hudu kafin Beijing.

Karin bayani