Takaitaccen tarihin Garba Lawal

Graba Lawal Hakkin mallakar hoto google
Image caption Graba Lawal na cikin tawagar da ta lashe lambar zinare a gasar Atlanta 1996.

An haifi Garba Lawal a ranar 22 ga watan Mayun1974 a garin Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya. Ya taba lashe lambar zinare a gasar wasanni ta Olympics.

A nan ne kuma ya yi rayuwarsa ta yarinta da samartaka.

Lawal ya fara taka leda a Najeriya a kulob din Ranchers Bess na garin Kaduna a gasar League ta Najeriya.

Ya kuma taka leda a kulob din Julius Berger na Legas a 1991.

A watan Nuwamban 1994 ne ya koma kulob din Esperence na kasar Tunisia.

Bayan gasar Olympics ta 1996 ne ya koma kasar Holland inda ya shafe shekaru yana yin wasa a kulob din Roda JC a gasar League ta kasar ta Holland.

Lambar yabo ta Olympics

Garba Lawal ya kuma taka leda a kasashen Bulgaria da Sweden da Portugal da kuma Girka.

Bayan ya kammala kwallo a nahiyar Turai, Garba Lawal, ya koma taka leda a kasar China tare da kulob din Changsha Ginde.

Ya kuma bugawa tawagar Super Eagles ta Najeriya kwallo a lokuta daban-daban.

Daga cikin gasar wasannin da ya halarta har da gasar wasanni ta Olympics a shekara ta 1996 inda ya lashe lambar zinare a fagen wasan kwallon kafa tare da tawagar Dream Team a birnin Atlanta na kasar Amurka.

Ya kuma halarci gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a shekarun 1998 da kuma 2002. Inda ya zira kwallo a wasan da Najeriya ta doke Spain da ci 3-2 a gasar ta 1998.

Ya kuma komawa gida Najeriya inda ya bugawa Julius Berger, sannan ya zamo dan wasa kuma koci a kulob din Lobi Stars.

A watan Agustan 2009, aka nada shi mataimakin koci na Lobi Stars. Sannan daga bisani ya zamo mai kula da jin dadin tawagar 'yan kwallon Najeriya ta 'yan kasa da shekaru 17.

A yanzu Garba Lawal yana zaune ne a mahaifarsa dake garin Kaduna a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Karin bayani