Mario Balotelli ya ce ba shi da aniyar barin City

Mario Balotelli
Image caption Mario Balotelli

Mario Balotelli ya ce ba shi da aniyar barin Manchester City a kakar bana

Mai horar da yan wasan City Roberto Mancini bayyana yiwuwar siyar da dan wasan gaban, bayan da aka kore shi a wasan su da Arsenal.

Tuni dai Mancini ya sauya matsayin sa, amma ya gargadi Balotelli da cewa, dole ne ya sauya halin sa idan ya na son ci gaba da kasancewa a kulob din.

City dai ba ta da aniyar tallata dan wasan, amma BBC ta fahimci cewa, kulob din shirye ya ke ya saurari tayi mai gamsarwa na siyan dan wasan a kakar bana.