Zanga zanga ta barke a Bahrain ana dab da fara gasar F1

F1 a Bahrain Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption F1 a Bahrain

Kwanaki kalilan kafin fara daya daga cikin manyan wasannin, gasar tseren motoci ta Formula One, rahotanni na nuna cewa jamian tsaro sun jefa gurneti na bogi don tarwatsa masu zanga zangar adawa da gwamnati.

Babu wani rahoton da ya nuna cewa akwai wanda ya jikkata, inda jamian tsaro suka kora masu zanga zangar.

Tashe tashen hankulan dai sun kai ga soke gasar tseren motocin ta Formula One a bara.

Tuni dai hukumar kula da tseren motocin FIA, ta yanke shawarar shiga gasar a karshen mako.

Karin bayani