Djokovic da Nadal sun tsallake zuwa zagaye na ukku

Novak Djokovic Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Novak Djokovic

Dan wasan Tennis na daya a duniya Novak Djokovic ya bude wasan sa na farko a gasar zakarun Tennis na Monte Carlo inda ya doke Andreas Seppi cikin sauki.

Dan shekaru 24 a duniya, Djokovic ya nuna kwarewa a fitowar sa ta farko a kakar wasannin Tennis na turbaya.

Shi ma Rafael Nadal mai rike da kambun a halin yanzu, ya doke Jarkko Nieminen dan kasar Finland a tirmi biyu na wasan a jere.

Shi dai Nadal, wannan ce fitowar sa ta farko tun bayan da ya janye daga wasan zakaru na Miami a sabili da rauni a gwiwar sa.

Karin bayani