An yi janaizar dan wasan Italiya da ya rasu a filin wasa

Piermario Morosini Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Piermario Morosini

Dubban masu alhini ne suka hadu a titunan Bergamo na kasar Italiya, don janaizar dan wasan kwalon kafar nan Piermario , wanda ya yanke jiki ya fadi ya rasu a cikin wasan rukuni na biyu na Italiya cikin karshen makon da ya gabata.

Masu sha'awar wasan kwallon kafar sun rika ajiye firanni da kyallaye da alluna don tunawa da Morisini, wanda ya rasu ya na da shekaru 25 a duniya.

Shi dai Piermario Morosini, ya rasu ne ya na yi wa kulob din Livorno wasa.

An bada umurnin yin wasu karin gwaje gwaje, bayan da bincike na farko ya kasa tabbatar da musabbabin mutuwar sa.

Karin bayani