Manchester City na rufe gibin da ke tsakaninta da United

Hakkin mallakar hoto AFP

Manchester City na rufe gibin yawan maki dake tsakaninta da United mai jagoranci a gasar Premier inda ta bi Wolves har gida ta lallasa da ci biyu da nema.

A yanzu haka dai maki uku ne tsakanin kungiyoyin biyu, bayan da Everton ta rike United a Old Trafford inda su ka tashi hudu da hadu.

Manchester City da United za su hadu ne a filin Etihad a karshen mako mai zuwa.

Sergio Aguero ne ya zura kwallon farko a ragar Wolves ana minti 27 da bakwai a wasan.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci ne kuma, Samir Nasri ya kara zura kwallo a ragar Wolves ana mintin 74 da wasan.

Da wannan wasan dai an ragewa Wolves matsayi kenan domin ba za ta damu damar buga gasar Premier a badi ba.