An dakatar da kwallon kafa a Masar

Hakkin mallakar hoto 1

Mahukunta a kasar Masar sun dakatar da duk wata gasar kwallon kafa a kasar saboda fargabar rashin tsaro musamman ma a filin wasanni.

Hakan na nufin ba za'a sake taka leda ba a kasar ba a kakar wasa na bana.

An dai dakatar gasar League a Masar ne bayan tashin hankalin da ya auku a lokacin wani wasa a Port Sa'id a watan Fabrairu inda kusan sama da mutane 74 su ka rasa rayukansu.

Ma'ikatar harkokin cikin gidan kasar dai ta ce tana son an kammala shari'ar tashin hankalin da ya auku ne, kafin a dawo taka leda.

Ana dai tuhumar mutane 75 da rura wutan rikicin.

Hukumar kwallon kasar dai ta ce za ta daukaka kara game da batun ga gwamnatin mulkin sojin kasar.