Ferguson na jiran wasan 'yan gida daya mafi girma

Image caption Alex Ferguson

Sir Alex Ferguson ya ce Manchester United za ta buga wasan 'yan gida daya mafi girma da Manchester City a filin Etihad a ranar Litinin mai zuwa.

A yanzu haka dai maki uku ne ke tsakanin Manchester United mai jagoranci a gasar ta Premier da kuma Manchester City da ke biye da ita, bayan United ta buga kunen doki da Everton inda su ka tashi hudu da hudu.

Manchester City dai ta doke Wolves da kwallaye biyu da nema.

Idan har dakarun Roberto Mancini suka doke United a ranar Litinin mai zuwa City ce, za ta dare a kan tebur saboda ta fi yawan kwallaye da ta zura a ragar abokan hammayar ta.

Ferguson ya ce: "Muna bukatar sakamako mai kyau. Wasan 'yan gida daya ne dake da mahimmanci matukka."

A wasan farko da kungiyoyin biyu su ka buga, City ce ta yi galaba a kan United a filin Old Trafford da ci shida da daya.

Ya kara da cewa: "Wannan wasan 'yan gida dayan duk ya fi muhimmaci a tarihi na a kwallon kafa. Zamu yi tattaki filinsu kuma mu tabbatar munyi abun da ya kamata domin samun nasara."

"Babu abun da zai sa ba zamu yi nasara ba. Ana ganin idan City ta lashe wasan da zamu buga za ta dauki kofi.. Ina ganin muma haka batun yake."