Everton ta rike Manchester United

Image caption 'Yan wasan Everton suna murnar zura kwallo

Kungiyar Manchester United ta fuskanci koma baya a kokarinta na lashe gasar Premier ta bana inda ta tashi hudu da hudu a wasa da ta buga da Everton a filin Old Trafford.

Dan wasan Everton Jelavic ne ya fara zura kwallon farko a ragar United sanan Wayne Rooney ya fanshe kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci ne kuma Danny Welbeck da Nani su ka zura kwallaye biyu a ragar Everton sanan kuma Marouane Fellaini ya fanshe daya.

Ana cikin hakan ne kuma Rooney ya kara kwallo a ragar Everton wanda ya sa wasan ya koma hudu da biyu.

Amma Everton ta nuna bajinta inda ta dawo da karfi a yayinda Jelavic da Steven Pienaar su ka fanshe kwallaye.

Manchester United dai ta yi ta kai hare-hare, amma mai tsaron gidan Everton Tim Howard bai bari an zura kwallo a ragarsa ba.