Van Persie ne gwarzon dan wasan PFA na bana

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Robin van Persie

Kungiyar kwararun 'yan wasa a Ingila ta bayyana Robin van Persie a matsayin gwarzon dan wasan kwallon kafa na bana a Ingila.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 28 ya zura kwallaye 38 a kakar wasa na bana.

Dan kasar Holland din ne yafi zura yawan kwallaye a gasar Premier a bana.

Van Persie ya ce; A gaskiya ina matukar farin cikin yadda abokan hammayar mu su ka nuna min kauna da wannan karamci."

Van Persie, ya taimakawa abokan wasansa na Arsenal shima dai ya yaba da irin kokarin da suke yi na taimaka masa a filin wasa.

"Idan ba dan su ba, ai da ban samu irin wannan karamci ba." In ji Van Persie.

Dan wasan Tottenham Kyle Walker ne kuma ya samu kyautar gwarzon matashi dan kwallon bana.