Murray ya doke Stakhovsky a gasar Barcelona Open

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Andy Murray

Dan wasan Tennis din Burtaniya Andy Murray ya doke Sergiy Stakhovsky da maki 6-3 da kuma 6-2 a wasan zagaye na biyu a gasar Tennis ta Barcelona Open.

Murray wanda shine na hudu a duniya, ya fuskanci wasu 'yan matsaloli a farkon wasan amma daga baya ya dawo da karfinsa ya doke Stakhovsky a minti 78.

Murray ya yi nasara ne a wasan bayan kashin da ya sha a hannun Tomas Berdych a wasan gab da kusa da na karshe a gasar Monte Carlo Masters da aka kammala a a karshen makon da ya gabata.

A yanzu haka dai Murray zai hadu ne da Robin Haase ko kuma Santiago Giraldo a wasan zagaye na hudu.