Barca za ta sauya yadda take taka leda- Guardiola

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kocin Barcelona Pep Guardiola

Kocin Barcelona, Pep Guardiola ya ce kashin da kungiyarshi ta sha a hannu Chelsea zai sa kungiyar ta sauya yadda take taka leda a nan gaba.

Guardiola dai ya ce Barcelona ta taka rawar gani sosai a wasan da ta buga da Chelsea.

"Na koya musu ko da yaushe su rika kai hare-hare a koda yaushe." In ji Guardiola.

"Ina ganin kashin da muka sha abu ne da ya kamata muyi koyi da shi nan gaba, mu duba yadda zamu sauya yadda mu ke kai hari."

Kocin mai shekarun haihuwa 41 ya ce zai yanke shawarar ko zai sabonta kwantaraginsa da Barcelona cikin wasu 'yan kwanaki.