Bayern Munich ta fidda Real Madrid

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan wasan Bayern Munich na murnar zura kwallo

Bayern Munich ta tsallake zuwa wasan karshe a gasar zakarun Turai bayan ta doke Real Madrid a filin Banabu a bugun daga kai sai mai tsaron gida da ci uku da daya.

An dai tashi wasan ne kafin a kai bugun fenarity Madrid na da kwallaye biyu Bayern Munich na da kwallo daya.

A wasan farko da kungiyoyin biyu su ka buga a Jamus a makon da ya gabata, Bayern Munich ce ta yi galaba a kan Real Madrid da ci biyu da daya a filin Alianz arena.

Christiano Ronaldo ne ya ci kwallaye biyu a wasan sannan Robben ya farkewa Bayen Munich kwallo daya.

Christiano Ronaldo da Kaka da kuma Sergio Ramos ne su ka bararwa Madrid kwallayen ta a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Sannan kuma Philip Lahm da Toni Kross su ka bararwa Bayern Munich na ta kwallayen .

Bastian Schweinsteiger ne dai ya zura kwallon da ya ba Bayern Munich nasara.

Bayern Munich dai za ta buga wasan karshe ne a filinta da Chelsea a watan gobe.