'Ya kamata Di Matteo ya ci gaba da zama a Chelsea'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Roberto Di Matteo

Tsohon Kocin Chelsea, Avram Grant, ya ce ya kamata, kocin wucin gadin Chelsea, Roberto di Matteo ya ci gaba da zama a Chelsea na tsawon shekara daya.

Chelsea da 'yan wasan goma ne ta doke Barcelona bayan kungiyoyin biyu sun tashi biyu da biyu abun da ya ba Chelsea nasara uku da biyu kenan saboda nasarar da ta yi a filin Stamford Bridge da ci daya mai ban haushi.

Grant, wanda aka sallama a Chelsea bayan ya kai kungiyar wasan karshe a gasar zakarun Turai ta shekara ta 2008 ya ce Roman Abramovich ya na da wuyan sha'ina saboda da wuya a san manufarsa.

"Ina ganin Roberto na bukatar shekara daya a kungiyar, amma sai yadda Abramovich ya yi saboda ya a wuyan sha'ani."

An dai nada Di Matteo kocin wucin gadi har zuwa karshen kakar wasan bana, bayan da aka sallami Andre Villas-Boas a watan Maris.

Grant ya kamata a ce Abramovich ya amince da irin rawar da Di Matteo ya taka a yayinda kungiyar ta kai ga wasan karshe a gasar zakarun Turai da kuma gasar cin kofin FA.

"Ya sallami masu horadda da 'yan wasa da dama, amma a lokacin kungiyar na fuskantantar matsaloli, sai dai yanzu kungiyar na kan ganiyar ta ne." In ji Grant.