Guardiola na gab da barin Barcelona

Hakkin mallakar hoto Getty

Kocin Barcelona Pep Guardiola na shirin ajiye aikinsa na horadda da kungiyar idan kwantaraginsa da kungiyar ya kare a karshen kakar wasa na bana.

Kocin mai shekarun haihuwa 41 zai bayyana aniyarsa a wani taron manema labarai a ranar Juma'a.

Idan ba wai Guardiola ya sauya ra'ayinsa ba, zai bar kungiyar da ya jagoranta zuwa lashe gasar zakarun Turai guda biyu.

Kocin zai gana da 'yan wasansa a ranar juma'a da safe kafin ya bayyana aniyarsa da rana.

Rahotanni na cewa dai Guardiola zai dauki dogon hutu daga harkar kwallon kafa idan ya ajiye aikinsa.

Guardiola ya kwashe kusan sa'o'i uku yana tattaunawa da Shugaban Barcelona Sandro Rossell a ranar Litinin da safe game da makomarsa.