Terry zai iya daga kofin gasar zakarun Turai

Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumar kula da kwallon kafa a Turai wato UEFA ta ce kyaftin din Chelsea da aka dakatar John Terry, zai iya daga kofin gasar zakarun Turai idan Chelsea ta iya doke Bayern Munich.

An dai dakatar da Terry ne daga buga wasan karshe bayan jan katin da aka nuna masa a wasan da Chelsea ta buga da Barcelona a bugu na biyu.

Dokar Uefa dai ta hana 'yan wasan da aka dakatar su zauna a kan benci a wasa na gaba.

Kuma hukumar ta ce ba za ta sauya dokar ta ba domin barin 'yan wasa shida na Chelsea da aka dakatar su samu buga wasan karshe ba.

A yanzu haka dai Terry zai kalli wasan ne cikin 'yan kallo, tare da Raul Meireles da Ramires da kuma Branislav Ivanovic duk da aka dakatar bayan katin da su ka samu a wasa da Barcelona.

Ita ma dai Bayern Munich ba za ta samu amfani da Luiz Gustavo da David Alaba da kuma Holger Badstuber ba saboda katin gargadin da aka nuna musu a wasan da kungiyar ta buga Real Madrid.