A Najeriya, an dakatar da gidan kallo

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jonathan a inda aka sa bam a kasar

A Najeriya, Hukumomi sun dakatar da gidajen kallon wasannin kwallon kafa a Jos babban birnin Jihar Plateau dake arewacin kasar bayan da yan Kungiyar Boko Haram suka kai hari wani gidan kallo.

Mutane tara dai sun ji rauni a harin da aka kai ranar Talata a wani gidan kallon wasa yayinda ake kallon wasan Chelsea da Barcelona.

Jami'an tsaro na yan sanda sun bada sanarwar cewa babu ranar bude gidajen kallon, abunda suka ce sunyi haka ne don kare rayukan masu son kwallon kafa.

Sai dai masu gidajen kallon na ganin haramta musu sana'ar tasu tamkar hana su samun kudaden shiga ne; a ganinsu me yasa ba za'a basu tsaro ba a maimakon a dakatar dasu.

Karin bayani