Pierre Lechantre ya zama Kociyan Senegal

Image caption Pierre Lechantre

A Kasar Senegal kuwa, tsohon wanda ya samu nasarar cin kofin Nahiyar Afrika ne Pierre Lechantre ya zama sabon mai bada horo na Senegal.

Lechantre, ya maye gurbin Amara Traore wanda aka yi awon gaba dashi bayan rashin katabus da yayi a gasar cin kofin nahiyar afrika wannan shekarar.

Kulab din Teranga Lions, na daga cikin wadanda ake ganin za suyi rawar gani kafin a fara gasar amma aka lalla sa su a duka wasannin su uku na zagaye na farkon gasar.

Sabon mai bada horon mai shekaru 62, ya jagoranci kasar Kamaru a gasar cin kofin Afrika na shekara ta dubu biyu da kuma wasannin Olympics.

Karin bayani