Redknapp, ya yi fatan alheri ga Roy

Image caption Redknapp

Kochiyan kungiyar kwallon kafa ta Totteham, Harry Redknapp, yayi fatan alheri ga Roy Hodgson kan matsayin da ake gab da nada shi a matsayin kochiyan Ingila.

Redknapp dai ya shaidawa Bbc cewa ba shi da rashin jituwa da Roy, ya ce baya rike mutum a zuciyarsa.

Redknapp dai shine wanda akai ta dangantawa da mukamin kafin Kungiyar kwallon kafan ta FA ta tuntubi Roy Hodgson.

A watan Fabrairu dai an ambato Redknapp na cewa mukamin na zama Kochiyan Ingila matsayin da kusan duk wani dan Ingila ke san cimmawa.

Karin bayani