Ferdinand ka iya bugawa Ingila gasar Turai

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Rio Ferdinand

Kochiyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Sir Alex ferguson ya na goyan bayan Ferdinand ya zama ya samu shiga tawagar yan wasan Ingila a gasar cin kofin nahiyar Turai.

Ferguson ya ce namijin kokari da yayi a kakar wasanni shine yasa sanya shi a cikin yan wasan zai yi amfani sosai, ya kara da cewa goge wa za ta yi amfani sosai a gasar.

Dan wasan dai mai shekaru 33 bai bugawa kasar sa wasa ba tun wasan neman futowa gasar da kungiyar kwallon kafa ta Switzerland a watan Yuni.

Sabon kochiyan Ingila Roy Hodgson ya ce zai magana da Ferdinand kan shigo dashi cikin tawagar yan wasan.

Karin bayani