Netherlands za ta kauracewa gasar kwallo

Ministan harkokin wajen Netherlands, Uri Rosenthal Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ministan harkokin wajen Netherlands, Uri Rosenthal

Ministan harkokin wajen Netherlands ya shaidawa BBC cewa kasarsa za ta kauracewa gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar Turai na shekarar 2012.

Mr. Uri Rosenthal yace Netherlands za ta kauracewa gasar da za'a buga a Ukrain, muddin ba'a daian muzgunawa shugabar 'yar adawar dake kurkuku ba.

Yulia Tymoshenko wacce ke yajin cin abinci ta yi korafin cewa ana dukanta a gidan kaso.

Wasu kasashen Turai da dama na tunanin kauracewa gasar suma.